Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiINEC ta sauya ranar zaben jihar Osun

INEC ta sauya ranar zaben jihar Osun

Hukumar INEC ta sanar da yin gyara a jadawalin kamfen ɗin zaɓen gwamnan jihar Osun mai zuwa, bayan da aka sauya ranar gudanar da zaɓen jihar.

Hukumar INEC ta sanar da yin gyara a jadawalin kamfen ɗin zaɓen gwamnan jihar Osun mai zuwa, bayan da aka sauya ranar gudanar da zaɓen jihar.

A baya, a ranar 26 ga Fabrairu 2026, INEC ta fitar da sabon jadawalin zaɓen 2027, inda ta matsar da zaɓen gwamnan Osun da mako guda, daga ranar 8 ga Agusta zuwa 15 ga Agusta, 2026.

A wata sanarwa da Kwamishinan ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa bayanai da ilimantar da masu zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar, ya bayyana cewa wannan sauyi ya shafi ranar ƙarshe ta kamfen ga jam’iyyun siyasa.

Ya ce: “Saboda wannan gyara, ranar ƙarshe ta kamfen ga jam’iyyun siyasa yanzu ita ce ƙarfe 12 na dare ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, bisa tanadin Sashe na 98(1) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya tanadi cewa dole ne a dakatar da kamfen sa’o’i 24 kafin ranar zaɓe.”

Hukumar ta buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su bi sabon jadawalin da aka fitar.
Ta kuma jaddada kudurinta na gudanar da zaɓe na gaskiya, adalci da sahihanci, tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaɓe cikin gaskiya da kowa ya amince da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments