Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMajalisar Ɗinkin Duniya ta ƙirƙiri manhajar da za ta magance matsalar ƙarancin...

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙirƙiri manhajar da za ta magance matsalar ƙarancin abinci a duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta fito da wani sabon shiri da ake sa ran zai taimaka wajen warware matsalar abinci.

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, WFO ya ƙaddamar da wani shafi da ke amfani da fasahar AI, domin ganowa da kuma magance matsalar yunwa a fadin sama da kasashe 50.

Babbar Daraktar hukumar, Cindy McCain, ta ce shafin, mai suna HungerMap Live – zai rika samar da bayanai kai tsaye a lokacin da abubuwa ke faruwa, tare da bayar da hasashe, da nufin ingantawa da kuma hanzarta ayyukan samar da abinci.

Hukumar da ke fitar da bayanai kan wuraren da aka fi fama da yunwa ta duniya, IPC, ta ce an ƙaddamar da shafin a kan gaɓa kasancewar an yi ne a daidai lokacin da aka samu karuwar matsalar ƙarancin abinci sosai a duniya, inda aka samu alkaluman da ba a taɓa samu ba na yawan mutanen da ke fama da yunwa a shekarun nan.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments