Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiAn fara hasashe wanda jam’iyyar ADC za ta tsayar takara a zaɓen...

An fara hasashe wanda jam’iyyar ADC za ta tsayar takara a zaɓen 2027

Rahotanni na nuni da yiwuwar wanda zai zama ɗan takarar ADC a zaɓen 2027.

Wani jigo a jam’iyyar PDP, Segun Showunmi, ya yi magana kan dan takarar da zai samu tikitin ADC a zaben shugaban kasa na 2027.

Segun Showunmi ya bayyana kwarin gwiwa cewa Atiku Abubakar ne zai lashe tikitin takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar ADC gabanin zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa Segun Showunmi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2026.

Showunmi ya bayyana dalla-dalla cewa Atiku yana da duk wani karsashi na zama ɗan takarar jam’iyyar.

Ya ce babu ko shakka a ransa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai samu tikitin ADC, yana mai nuni da ƙarfinsa na siyasa da kuma shirye-shiryensa na shiga tseren.

Sai dai, ya lura cewa Atiku na iya fuskantar takara mai zafi daga tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya bayyana a matsayin babban abokin hamayyar Atiku a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da ake sa rai.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments