Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƳan sanda sun daƙile yunkurin kai harin bom a jihar Ondo

Ƴan sanda sun daƙile yunkurin kai harin bom a jihar Ondo

Yan sandan jihar Ondo sun dakile wani yunkurin tayar da bam tare da kama mutane shida da ake zargi da shirin kai hari kan muhimman wuraren gwamnati.

’Yan sandan jihar Ondo sun dakile wani yunkurin tayar da bam tare da kama mutane shida da ake zargi da shirin kai hari kan muhimman wuraren gwamnati.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Adebowale Lawal, ya bayyana cewa an gudanar da wannan samame ne a ranar 15 ga Afrilu, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri kan wata ƙungiyar masu aikata laifi da ke aiki a jihohi da dama. Ya ce jami’an tsaro sun yi gaggawar kai farmaki wurin da aka gano, inda suka cafke mutanen kafin su aiwatar da shirin su.

Bincike da aka yi a wani gida a unguwar Oke-Odu da ke Akure ya gano kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen kera bam na hannu, tare da wasu abubuwa kamar kwalabe 217, buhun sukari, wayoyi 17, kwamfutoci guda biyu, kuɗi N187,000, babura da kuma wasu kayan tsafe-tsafe.

An bayyana sunayen waɗanda aka kama da Adekunle Prosper, Ojo Olumide, Tope Kolawole, Ahmed Salihu, Bolaji Adebowale da Gbadebo Abidemi. Rahotanni sun nuna cewa suna shirin haɗa na’urorin fashewa domin kai hari a wurare masu muhimmanci, inda aka kuma gano takardu da ke nuna wuraren da ake niyyar kai harin.

Kwamishinan ya shawarci masu gidaje da su riƙa bincikar masu haya sosai, domin wasu na amfani da gidaje wajen aikata laifi.

A wani samame daban kuma, ’yan sanda sun kama wasu mutane goma da ake zargi da harkar ƙungiyoyin asiri a Ondo Town. Daga cikinsu akwai wani da ake zargi shugaban ƙungiyar ne, wanda ake nema ruwa a jallo kan wasu hare-hare da suka gabata.

An samu makamai da suka haɗa da bindiga, adda, gatari, alamomin ƙungiya da kuma tsafe-tsafe a wurin. ’Yan sanda sun tabbatar da cewa duk waɗanda aka kama suna tsare, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments