6
Kotun Tarayya da ke Kaduna ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a shari’ar cin hanci da rashawa da ICPC ta shigar a kansa.
Alƙali Rilwanu Aikawa ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan dage sauraron shari’ar daga 1 ga Afrilu zuwa 14 ga Afrilu 2026 domin nazarin hujjojin ɓangarorin biyu.
Kotun ta amince a sake shi da belin naira miliyan 200, amma ta umurci ya ci gaba da kasancewa a hannun ICPC har sai ya cika dukkan sharuɗɗan belin.
Daga cikin sharuɗɗan akwai hana shi yin wata magana a bainar jama’a kan shari’ar, da kuma wajabcin halartar duk zaman kotu. Lauyan sa, Ubong Akpan, bai yi tsokaci ba bayan shari’ar.
Wani makusancin sa, Hayatudeen Lawal Makarfi, ya bayyana cewa akwai kusan sharuɗɗa guda 10 da aka gindaya, ciki har da samar da wanda zai tsaya masa mai kadarar fili da kuma mai sarauta.
Ɗansa, Bello El-Rufai, ya tabbatar da cewa an ba mahaifinsa beli, tare da nuna godiya ga kotu da kuma kira ga mutunta tsarin shari’a.
Tun da farko, ICPC ta gurfanar da El-Rufai bisa tuhume-tuhume guda tara da suka haɗa da zargin karkatar da kudade, cin zarafin ofis, da kuma bada fa’ida ga kansa.
Ana zargin ya sa gwamnatin jihar ta fitar da kimanin Naira biliyan 11 zuwa wani kamfani da ba a yi rajista ba domin aikin layin dogo wanda ba a taɓa aiwatarwa ba. Haka kuma ana zargin ya karɓi kusan Naira miliyan 289.8 a matsayin alawus na barin aiki, wanda ya zarce abin da doka ta amince da shi.
Bugu da ƙari, ana zargin ya karkatar da sama da Dala miliyan 1.08 daga rancen World Bank, da kuma ba da kwangilar CCTV ta naira biliyan 4.6 ba bisa ƙa’ida ba.
Sai dai El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.
Duk da an ba shi beli, wani lauya mai suna El Zubair Abubakar ya bayyana cewa ba zai fito nan take ba saboda yana fuskantar wata shari’a daban a wata kotu a Kaduna wacce ba ta ba shi beli ba tukuna.
Saboda haka, zai ci gaba da zama a tsare har sai an ba shi beli a waccan shari’ar kuma ya cika dukkan sharuɗɗan da kotunan biyu suka gindaya.