Aƙalla mutane 56, galibinsu ‘yan kasuwa, ana fargabar sun rasa rayukansu, yayin da wasu 14 ke kwance a asibiti sakamakon wani harin sama da aka kai kasuwar mako-mako a kan iyakar jihohin Borno da Yobe.
Lamarin ya faru ne a kasuwar Jilli, da ke tsakanin ƙananan hukumomin Gubio da Geidam, a ranar Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne a yayin wani farmakin soji da ke farautar ‘yan Boko Haram, amma harin ya kuskure tare da nufar kasuwar, ya kuma haddasa jikkata gami da rasa rayukan ‘yan kasuwa da masu saye daga yankuna da dama kamar Gubio, Chiweram da Benisheikh a Borno, da kuma Gurokayeya da Geidam a Yobe.
Majiyoyi sun ce jirgin yaƙi yana bin wasu da ake zargin ‘yan tada ƙayar baya ne da suka zo kasuwar domin karɓar haraji daga ‘yan kasuwa da kuma samun kayayyaki, amma harin ya sauka kan fararen hula maimakon waɗanda ake nema.
Wani shaidan gani da ido ya ce an tabbatar da mutuwar mutane 56, yayin da wasu 14 ke jinya a Asibitin Kwararru na Geidam. Ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 2:46 na rana yayin da kasuwanci ke gudana.
“Na ga gawarwaki 56 da idona, kuma na taimaka wajen kai wasu biyu da suka jikkata asibiti. Ina ganin adadin na iya ƙaruwa saboda ana ci gaba da gano wasu
gawarwaki,” in ji shi.
Hakimin mazabar Fichimaram, Malam Lawan Zanna, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sama da mutane 20 aka kwantar a asibiti, wasu kuma aka tura zuwa asibitin koyarwa na Damaturu.
Shi ma mai ba gwamnan Yobe shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Abdulsalam Dahiru mai ritaya, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ya auku ne a yankin Borno.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar sojin saman Najeriya kan wannan hari.