Rahotanni sun cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Kano sun mika sunayen mutane uku ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya duba kuma ya zabi guda a cikinsu domin maye gurbin mukamin mataimakin gwamna da shi.
An cimma wannan matsaya ne bayan wani taro da aka gudanar a ranar Asabar, bayan tattaunawa da shawarwari tsakanin shugabannin jam’iyyar.
Taron wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranta, ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar.
A karshen taron, an mika sunan tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum da tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi, Murtala Sule Garo; da kuma tsohon sakataren gwamnatin Kano Rabiu Suleiman Bichi domin daukar daya a cikinsu.
Kujerar mataimakin gwamnan ta zama ba kowa ne tun bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, sakamakon barazanar tsige shi da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi bisa zargin almundahar kudade.
Kafin wannan mataki na masu ruwa da tsaki, ana ta rade-radin cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Isma’il Falgore da Murtala Sule Garo ne ke kan gaba wajen neman mukamin.
Sai dai sabon ci gaban ya nuna cewa an karkata zuwa yin karin shawarwari a cikin jam’iyyar kafin daukar mataki na karshe.