Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƳan bindiga sun kakabawa al’umma harajin shanu 70 da tumaki 1,000 a...

Ƴan bindiga sun kakabawa al’umma harajin shanu 70 da tumaki 1,000 a Kastina

An ruwaito cewa ƴan bindiga na karɓar shanu da sauran dabbobi a matsayin haraji daga mazauna yankuna.

Yan bindiga sun bukaci wasu yan ƙauyuka a jihar Katsina da su biya haraji da dabbobi saboda gudun kai masu farmaki kamar yadda aka saba.

Maharan sun bukaci shanu 700 da tumaki 1,000 daga wasu kauyuka uku a karamar hukumar Kankia da ke Katsina, suna barazanar kai hari idan ba a biya ba.

An isar da sakonnin bukatar ta hanyar wasiku zuwa kauyukan Rimaye da Sukunturi ranar 6 ga Afrilun 2026, inda aka bai wa mazauna wa’adin kwanaki hudu.

Wani mazaunin yankin, Malam Ahmadu Kankia, ya ce wannan wasika ta haddasa tsoro, inda jama’a daga Kunduru, Sukunturi, Tsa da Magam suka tsere daga gidajensu.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments