Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnan Kano ya ɗauki alƙawarin kawo karshen matsalar ruwa a jihar

Gwamnan Kano ya ɗauki alƙawarin kawo karshen matsalar ruwa a jihar

Gwamnan Kano ya tabbatar da cewa za a magance matsalar ruwan sha domin al’ummar jihar su samu sauƙi.

Gwamnan Kano ya jaddada cewa gwamnatinsa na da ƙudirin kawo ƙarshen matsalar ruwa a Kano.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Mustapha Muhammad, ya fitar.

A yayin rangadin, an gano matsaloli da suka hada da zubewar ruwa a bututu, lalacewar wasu injuna da kuma tsufan wasu kayayyaki, inda gwamnan ya yi alkawarin daukar matakan gyara da sabunta wasu.

Da yake zantawa da manema labarai, Gwamna Abba ya jaddada kudurin gwamnatin sa na gyara cibiyoyin tace ruwa da inganta samar da ruwa ga al’umma.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati za ta hada kai da kwararru daga kasar China domin tabbatar da samar da ruwan sha mai tsafta kuma wadatacce, yana mai cewa samar da ruwa mai kyau na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments