Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMalam Abduljabbar ya bukaci a sauya masa kurkuku daga Abuja

Malam Abduljabbar ya bukaci a sauya masa kurkuku daga Abuja

Sheikh Abduljabbar ya gabatar da ƙorafi ga hukumomi, yana mai neman a sauya masa gidan yari saboda halin da yake ciki a Abuja.

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da aka yanke wa hukuncin kisa bisa zargin batanci, ya shigar da kara yana neman a mayar da shi Kano daga gidan yarin Kuje a Abuja.

A cikin wani korafin da ya gabatar a gaban Kotun Daukaka Kara a Kano, mai dauke da kwanan wata 3 ga Afrilu, 2026, malamin ya ce sauya masa wuri zuwa Abuja ya hana shi samun muhimman takardun da yake bukata domin daukaka karar da ya shigar.

Rahotanni sun nuna cewa takardun, wadanda suka kunshi sama da shafuka 5,000 da suka kunshi bayanan shari’a da hujjojin da ya ce yana da su, suna gidan yarin Kurmawa lokacin da aka mayar da shi Kuje.

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya jaddada cewa yana bukatar tabbatar da cikakkun takardunsa kafin a ci gaba da sauraron shari’ar da ake.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments