Gwamnatin Jihar Jigawa ta kama malamai bakwai bisa zargin yin magudi a jarrabawar tantance kwarewa da aka gudanar ga sama da malamai 8,400 a fadin jihar.
An gudanar da wannan gwaji ne karkashin Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Jigawa domin inganta kwarewar malamai da kuma ingancin koyarwa a makarantun gwamnati.
Shugaban hukumar, Haruna Musa, ya bayyana cewa an mika malamai da ake zargi ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike.
Ya ce wannan jarrabawa, wadda ake kira Teacher Training Needs Assessment, an shirya ta ne domin gano gibin ilimi da kwarewar malamai tare da tsara horo na musamman a gare su.
Musa ya jaddada cewa wannan shiri ba wai kawai gwajin ilimi ba ne, har ila yau yana da nufin dawo da gaskiya da kwarewa a tsarin ilimi.
Ya kuma gargadi cewa magudi a jarrabawa, ko daga dalibai ko malamai, na lalata martabar bangaren ilimi kuma ba za a lamunta da shi ba.
Haka kuma ya yi gargadi kan rashin zuwa aiki da kuma shiga harkokin siyasa a lokacin aiki.
Hukumar ta ce wannan mataki zai zama darasi ga sauran malamai, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da tsaurara dokoki da ladabtarwa a bangaren ilimi.