Yan ta’adda sun kai hari wani ofishin ‘yan sanda a Arewa maso gabashin Najeriya a ranar Asabar, inda suka kashe ‘Yan sanda 4, sannan kuma suka kai hari wani sansanin ‘yan gudun hijira, kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta bayyana, a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙaruwa a hare-haren ta’addanci.
‘Yan sandan sun ce “ana zargin ‘yan ta’addan mambobin Boko Haram/Daesh ne suka kai hari hedikwatar ‘yan sandan Nganzai da nufin kwace garin”, wanda ke ƙasa da kilomita 100 arewa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno a Arewa maso gabas.
Kimanin makonni biyu da suka gabata, ‘yan ƙunar baƙin-wake uku sun tayar da bama-bamai a wata kasuwa mai cunkoso da wasu wurare a Maiduguri, inda suka kashe aƙalla mutane 23, a ɗaya daga cikin hare-hare mafi muni da aka gani a birnin cikin shekaru.
Jami’an tsaro da ke bakin aiki a harin na ranar Asabar “sun gwabza da maharan”, kamar yadda kakakin ‘Yan sanda ya bayyana a wata sanarwa, amma “jami’an ‘yansanda 4” sun mutu.