Farfesa Joash Amupitan, shugaban INEC, ya gargadi jam’iyyar ADC da ta dakatar da shirinta na gudanar da tarukan jam’iyya da babban taro na kasa, sakamakon rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar.
Bayan kotu ta yanke hukunci, INEC ta cire sunayen shugabannin ADC daga tsarin ta, tare da bayyana cewa ba za ta sa ido kan babban taron jam’iyyar ba idan rikicin bai lafa ba.
INEC ta kuma ce ba za ta sake amincewa da bangarori daban-daban a cikin jam’iyyar ba, bayan nazarin hukuncin kotun daukaka kara.
Sai dai kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar ba za ta dakatar da shirinta ba, yana mai cewa sun bi dukkan ka’idoji, kuma za su ci gaba da gudanar da taruka da babban taro ko INEC ta halarta ko ba ta halarta ba.
Amma Amupitan yayi gargadin cewa idan aka ci gaba da irin wadannan matakai duk da umarnin kotu, hakan na iya jawo mummunan sakamako na shari’a.
Ya yi nuni da abin da ya faru a Jihohin Zamfara da Plateau, inda rashin bin umarnin kotu ya sa aka soke nasarar zabe, aka kuma bai wa wanda ya zo na biyu nasara.
Ya kara da cewa duk wanda ya saba wa umarnin kotu zai iya fuskantar irin wannan sakamako, yana mai gargadin cewa INEC ba ta son sake fadawa irin wannan matsala.