Kasa da sa’o’i 24 bayan ziyarar shugabannin jam’iyyar ADC a Jihar Bauchi, wata tawaga mai ƙarfi ta jam’iyya mai mulki ta APC ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ita ma ta kai ziyara a jihar inda ta yi ganawar sirri da Gwamna Bala Mohammed.
Rahotanni sun ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan ƙoƙarin shawo kan Gwamna Mohammed da kada ya sauya sheƙa zuwa ADC, a maimakon haka ya yi la’akari da komawa APC.
Gwamnan, a ƙarshen taron, ya shaida wa manema labarai cewa zai ɗauki mataki na ƙarshe kan sauya sheƙar nan ba da jimawa ba, inda ake sa ran zai fitar da sanarwa a hukumance nan da ranar Alhamis.