Rundunar ƴan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa Babban Sufeto Janar na ƴansanda, Olatunji Disu, ya bayar da umarnin rusa duka rundunonin hukuman ƴansanda na musamman a jihohin ƙasar ba.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Anthony Placid, ya fitar, rundunar ta bayyana cewa rahotannin sun jirkita umarnin da IGP ya bayar.
Sanarwar ta ce wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa Sufeto Janar ɗin ya umarci a rusa rundunonin musamman na ƴansanda da dama a faɗin ƙasar nan take, amma rundunar ta jaddada cewa wannan bayani ba daidai ba ce.
Rundunar ta ƙara da cewa, duk da damuwar jama’a kan yadda wasu daga cikin rundunonin ke aiki, IGP na ganin suna taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da aikata laifuka a Najeriya.
“IGP, wanda ya riƙe muƙamai daban-daban a faɗin ƙasar nan ya damu da yawaitar rundunoni na musamman na ƴansanda, wanda hakan na rage yawan jami’an da ke aiki a ofisoshin ƴansanda, tare da haifar da matsalolin da ke shafar martabar rundunar sakamakon wasu halaye marasa kyau na rundunonin da ba a kula da su sosai,” in ji sanarwar.
A cewar rundunar, wannan mataki zai taimaka wajen ƙara yawan jami’ai a ofisoshin ’yan sanda, domin ƙarfafa aikin tsaro a matakin ƙasa da kuma magance koke-koken jama’a kan wasu ayyukan da suka wuce gona da iri daga rundunonin musamman.