Majalisar dattawan jami’ar ce ta amince da wannan mataki a zamanta na 433 da aka gudanar a ranar 4 ga Maris, 2026, bayan binciken da kwamitin jami’ar kan matsalolin cancantar shiga jami’a ya gudanar.
A wata sanarwa da jami’ar ta fitar a mujallarta ta mako-mako, an bayyana cewa an kama ɗaliban da laifin gabatar da takardun bogi a lokacin da suke neman gurbin karatu.
Sanarwar ta ce: “Majalisar dattawan jami’ar Bayero Kano, a zamanta na 433 da aka yi ranar 4 ga Maris, 2026, ta amince da korar ɗalibai 171 saboda gabatar da takardun ƙarya wajen samun gurbin karatu.”
Jami’ar ta ƙara da cewa wannan laifi ya saba wa sashe na 20.7, rukuni na A (vii) na dokokin jarabawa da harkokin ilimi na jami’ar, wanda ya tanadi hukuncin kora ga duk wanda ya aikata irin wannan laifi.
Ta kuma bayyana cewa ɗaliban da aka kora sun fito daga sassa daban-daban da matakai daban-daban na karatu, inda ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin tsaftace bayanan ilimi na jami’ar.
A wani lamari makamancin haka, majalisar ta kuma amince da korar wani ɗalibi mai suna Yusuf Muhammad Sani daga sashen Injiniyan Gine-gine, bisa zargin kai hari ga masu sa ido yayin gudanar da jarabawa.
Jami’ar ta ce wannan lamari ya kawo cikas ga tafiyar da jarabawar tare da karya dokokin ladabtar da ɗalibai.
Hukumar jami’ar ta sake jaddada aniyarta na kare ingancin ilimi, tana mai gargadin cewa duk wanda ya karya dokokinta zai fuskanci hukunci mai tsauri.
Ta ƙara da cewa wannan korar ɗalibai da yawa wani babban gargadi ne ga ɗalibai na yanzu da masu shirin shiga jami’ar, cewa BUK ba ta yarda da magudi ko rashin ɗa’a a harkokin ilimi ba.