Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da harin bam a Maiduguri.

Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da harin bam a Maiduguri.

Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta nuna matuƙar damuwa kan hare-haren bam da suka girgiza Maiduguri, inda ta bayyana su a matsayin mummunan hari ga rayukan fararen hula.

Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta nuna matuƙar damuwa kan hare-haren bam da suka girgiza Maiduguri, inda ta bayyana su a matsayin mummunan hari ga rayukan fararen hula.

Fashewar ta auku ne a wurare uku a lokaci guda, ciki har da kusa da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da kuma Monday Market, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dama.

Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya miƙa ta’aziyya ga al’ummar Borno, tare da bayyana harin a matsayin yunƙurin jefa yankin cikin tsoro da tada zaune tsaye. Ya kuma jajanta wa waɗanda suka jikkata tare da yabawa jami’an tsaro da masu agaji kan gaggawar da suka yi wajen kai ɗauki.

Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnonin Arewa na haɗa kai da Gwamnatin Tarayya domin yaƙar ta’addanci, yana mai kira ga jama’a da su ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro. Ya kuma buƙaci a ƙara ƙoƙari wajen kamo masu hannu a harin, yana mai cewa dole ne a tsaya tsayin daka wajen kare zaman lafiyar yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments