Mutane sun shiga firgici bayan tashin bama-bamai a Maiduguri.
Mazauna birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sun shiga cikin firgici a yammacin ranar Litinin bayan jin ƙarar fashe-fashe masu ƙarfi a wurare da dama.
Ana zargin mayakan Boko Haram da dasa abubuwan fashewa na IED a wasu sassan tsohon birnin.
Wuraren da fashe-fashe suka shafa sun haɗa da ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), shatal-talen Monday Market, da kuma yankin Elkanemi.
Rahotanni sun ce an fara jin fashewar farko ne da misalin ƙarfe 7 na yamma, jim kaɗan bayan musulmi sun yi buda-baki.
Har yanzu ba a tabbatar ko akwai waɗanda suka rasa rayukansu ko suka jikkata ba sakamakon lamarin.
Wannan lamari ya faru ne ‘yan sa’o’i kaɗan bayan wasu ‘yan ta’adda sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke Ajilari, wani yanki a wajen Maiduguri.
Rahotanni sun ce maharan sun banka wa wurin wuta tare da dauke wata motar sintiri ta sojoji.
Sai dai dakarun sojoji sun samu nasarar daƙile harin, inda suka kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da wasu da dama suka tsere daga wurin da raunukan harbi.