Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiWasu fasinjoji sun jikkata a hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

Wasu fasinjoji sun jikkata a hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

Babban daraktan hukumar layin dogo na Najeriya, Kayode Opeifa ya tabbatar da aukuwar hatsarin jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Sai dai a zantawarsa da manema labarai, ya ce ba a samu rahoton asarar rayuka ba, amma an jikkata.

Hukumar da ke kula da layin dogo ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa wasu daga cikin fasinjoji sun samu rauni, bayan hatsarin da ya faru kusa da tashar jirgin ƙasa ta Asham a layin dogon Abuja zuwa Kaduna da safiyar yau.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar, babban daraktan hukumar NRC Kayode Opeifa ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe kuma ya shafi wani bangaren jirgi ne da ya bugi wanda ke gabansa, kamar yadda kafar talabijin ta Channels ta ƙasar ta ruwaito.

Opeifa ya tabbatar da cewa nan take aka garzaya da fasinjojin da suka ji raunin asibitin da ke kusa domin kula da su yayin da ya ƙara da cewa ba a rasa rai ba a hatsarin.

Darakatan na hukumar NRC ya kuma bayyana cewa nan take aka tayar da matakan agajin gaggawa kuma aka tura ma’aikata masu ruwa da tsaki inda lamarin ya auku.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments