Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeTrump ya fara neman taimakon manyan ƙasashen duniya kan Iran

Trump ya fara neman taimakon manyan ƙasashen duniya kan Iran

Iran ta ƙi ja da baya, Trump ya fara neman tallafin ƙasashen duniya.

Yayin da Iran ke ci gaba da hana manyan jiragen ruwa na dakon kaya wucewa ta mashigar ruwa ta Hormuz sakamakon rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin magana kan bude mashigar ruwa ta Hormuz wadda Iran ta kulle.

Donald Trump ya yi kira ga sauran ƙasashe a da su tura jiragen yaƙi na ruwa domin taimaka wa wajen tabbatar da tsaron mashigar ruwa Hormuz.

Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne a cikin sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social a ranar Asabar, 14 ga watan Maris 2026.

Kalaman na Trump na zuwa ne bayan Iran ta kulle mashigar ruwan wadda ta kasance babbar hanyar jigilar man fetur cga duniya sakamakom rikicin Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Trump ya ce ƙasashe da dama za su iya haɗa kai da Amurka domin buɗe wannan hanyar ruwa ga jiragen dakon kaya na ƙasa da ƙasa.

Sai dai Sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ci gaba da kulle mashigar ta Hormuz domin matsawa Amurka lamba kan yakin da take yi da kasarsa.

Mashigar Hormuz tana ɗaya daga cikin muhimman hanyayoyin safarar makamashi na duniya, inda ake gudanar da gagarumin wani kason jigilar man fetur na duniya.

Fiye da gangar mai miliyan 20 ne ke ratsawa ta mashigar kowace rana, kusan kashi ɗaya cikin biyar na abin da duniya ke amfani da shi gaba ɗaya.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments