Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya kafa kwamiti kan man fetur bayan da jama’a suka fara...

Tinubu ya kafa kwamiti kan man fetur bayan da jama’a suka fara korafi kan tsadar litar mai

‘Yan Najeriya na kuka kan tsadar litar mai, Tinubu ya kafa kwamiti kan fetur.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa wani kwamitin bincike da fasalta fannin man fetur na ƙasa domin samar da sabbin sauye-sauye a fannin.

Shugaban ya naɗa Mista Fola Adeola, fitaccen masanin harkar kuɗi kuma wanda ya kafa bankin GTB, a matsayin shugaban wannan kwamiti na musamman.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da kafa kwamitin a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Bayo Onanuga ya bayyana cewa wannan kwamiti zai yi aiki ne ba tare da tsoma bakin kowa ba domin samar da tsare-tsaren da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa.

Kwamitin ya ƙunshi kwararru kamar Ademola Adeyemi-Bero da Osagie Okunbor, waɗanda aka ɗora wa alhakin maida fannin man fetur na Najeriya ya zama mai gaskiya da kuma janyo hankalin masu zuba jari.

Babban burin wannan kwamiti dai shi ne buɗe hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma ƙarfafa matsayin Najeriya a fannin makamashi na duniya.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments