Wata gobara da ta tashi a daren Asabar ta lalata fiye da shaguna 10 a Kasuwar Terminus da ke Jos, a Jihar Plateau.
Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10:00 na dare, bayan da ‘yan kasuwa suka rufe shaguna suka tafi gida.
Lamarin ya faru ne watanni uku kacal bayan wata irin gobara ta dare da ta lalata wani bangare na kasuwar.
Rahotanni sun ce shaguna da dama sun kone ƙurmus. Kayayyaki irin su tufafi da takalma sun ƙone sun zama toka.
Har yanzu hukumomin kasuwar ba su tabbatar da abin da ya haddasa gobarar ba. Sai dai wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun yi zargin wutar lantarki ce.
Masu kashe gobara da jami’an agaji sun isa wurin da sauri, inda suka yi nasarar dakile wutar kafin ta bazu zuwa wasu sassan kasuwar.Wani shaidan gani da ido, Mista Silas Lawrenzo, ya ce hukumomin agaji da dama sun haɗa kai wajen kashe gobarar.Ya ce, “
Masu kashe gobara, daga ciki har da wata tawaga daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun yi aiki tare da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Plateau, da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da kuma Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Plateau wajen shawo kan lamarin.”
A cewarsa, saurin kawo agaji da haɗin gwiwar hukumomin ya taimaka wajen takaita ɓarnar tare da hana wutar bazuwa zuwa sauran sassan kasuwar da ake yawan harkokin kasuwanci a cikinta.
Rahotanni sun nuna cewa Kasuwar Terminus ta fuskanci gobara sau uku a cikin shekara guda, lamarin da ya lalata kayayyakin ‘yan kasuwa da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.