Ƙungiyar Hamas ta yi kira ga Iran da ta dakatar da kai hare-hare ƙasashen da ke makwabtaka da ita, inda ta ce Tehran nada haƙiƙin kare kanta daga hare-haren Isra’ila da Amurka.
A cikin wata sanarwa da Hamas ta fitar a yau Asabar, ta kuma buƙaci ƙasashe su ɗauki matakin kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a yankin gabas ta tsakiya, da aka faro a ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata.
A baya dai Hamas wacce ta kwashe sama da shekaru biyu tana yaƙi da Isra’ila, ta fitar da sanarwar da ke Allah wadai da kisan da aka yi wa Ali Khamenei jagoran addini na Iran, wanda ya kwashe shekaru ya na nuna goyon baya ga fafutukar da Falasɗinawa ke yi.
Wani jami’in Hamas ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran AFP cewa, ƙungiyar na nan na tattaunawa hukumomin Iran game da hare-haren da taka kai wa yankin.
Shugabannin Hamas sun tuntuɓi jami’an ƙasashe da dama da suka haɗa da Qatar da Turkiyya da kuma Iraƙi, inda suka buƙace su da su yi ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren Amurka da Isra’ila ke yi a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Duk da hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kai wa Iran, hakan bai dakatar da ita ba wajen maida martani ba a wasu muradun Amurkan da ke ƙasashe aƙalla 10 a yankin Gabas ta Tsakiya ba.