Sunday, October 18, 2026
HomeLafiyaNajeriya ta yi gargaɗi kan yaduwar cutar sankarau a wasu jihohi na...

Najeriya ta yi gargaɗi kan yaduwar cutar sankarau a wasu jihohi na Arewa

Ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta sanar da cewa akwai barazanar kamuwa da sankarau a wasu jihohin Arewa.

Najeriya ta yi gargaɗi kan haɗarin kamuwa da cutar sanƙarau a wasu jihohin Arewacin ƙasar.

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya NiMet ce ta fitar da sanarwar gargaɗi game da lafiyar jama’a inda ta ce akwai jihohin Arewacin ƙasar da dama da ke fuskantar ƙarin haɗarin kamuwa da cutar sankarau yayin da yanayin zafi ke ƙaruwa a sassan ƙasar.

A cikin wata sanarwa, hukumar ta bayyana cewa cutar sanƙarau wata mummunar cuta ce da ke shafar ƙwayoyin kariya da ke rufe

ƙwaƙwalwa da lakar baya, kuma galibi ƙwayar cutar Neisseria meningitidis ce ke haddasa ta.

NiMet ta kuma bayyana cewa cutar na yaɗuwa ta hanyar numfashi daga mutum zuwa mutum, musamman a wuraren da ake cunkoso ko kuma wuraren da iska ba ta shiga yadda ya kamata.

Hukumar ta bayyana Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe da Borno a matsayin jihohin da ke cikin babban haɗari na kamuwa da cutar.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments