Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKotu a jihar Ekiti ta yanke wa likitan bogi hukuncin kisa ta...

Kotu a jihar Ekiti ta yanke wa likitan bogi hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yanke wa wani mutum da ya riƙa bayyana kansa a matsayin likita hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an same shi da laifin kashe wata mata.

Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yanke wa wani mutum da ya riƙa bayyana kansa a matsayin likita hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an same shi da laifin kashe wata mata.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin mai suna Olatide Emmanuel, mai shekaru 48, ya buɗe wani asibiti a shekarar 2019 duk da cewa ba shi da cikakkiyar ƙwarewar likitanci.

Ana zarginsa da yi wa wata mata mai suna Bosede Falade tiyatar haihuwa ta, wadda daga bisani ta rasu sakamakon matsalolin da suka biyo bayan aikin.

A lokacin shari’ar, mai gabatar da ƙara ya gabatar da shaidu da hujjoji da suka haɗa da bayanan likitoci da hotuna, inda kotu ta tabbatar cewa mutumin ya yi aikin likitanci ba tare da cancanta ba, lamarin da ya haifar da mutuwar matar.

A hukuncin da ya yanke, alkalin kotun ya bayyana cewa aikin da mutumin ya yi ya nuna sakaci da rashin kula da rayuwar ɗan Adam. Saboda haka kotun ta same shi da laifin kisan kai tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments