Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiRasha na cikin ƙasashen da suka fi cin moriyar yaƙin Gabas ta...

Rasha na cikin ƙasashen da suka fi cin moriyar yaƙin Gabas ta Tsakiya

Rahoto ya nuna Rasha na cikin manyan ƙasashen da ke samun riba daga rikicin Gabas ta Tsakiya.

Wasu alƙalman Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa ƙasar Rasha ce ke samun nasara a yaƙin da yanzu haka ake gwabzawa a tsakanin haɗakar Amurka da Isra’ila da kuma Iran.

Wannan dai na zuwa ne bayan da ake hasashen cewa Iran ta amincewa jiragen man Rasha kaɗai su ratsawa ta mashigin Hormuz da ta rufe, yayinda ita kuma Rahsa ke taimaka mata da bayanan sirri.

Baya ga haka kuma akwai yadda matsin lamba ya tilastawa Amurka sassauta wa Rasha takunkuman da ta sanya mata na cinikin man fetur, tun bayan da ta ƙaddamar da yaƙi kan Ukraine.

Da yake bayani shugaban majalisar Tarayyar Turai Antonio Costa, ya ce wannan yaƙi ya bai wa Rasha damar shan iska, kan matsin da ta shiga na hana kowacce ƙasar sayen manta.

Tuni dai Rasha ta miƙawa ƙasashen Turai tayin sayar musu da man fetur da sauran albarkatun makamashi idan suna da buƙata, kuma ana hasashen cewa basu da zaɓi illa saye a farashi mai tsadar gaske.

Tun ba yau ba ana ganin Rasha wata babbar aminiya ce ga Iran, a don haka ne Rahsa ta yi amfani da damar da ta samu sakamakon wannan yaƙi wajen shan iska da kuma cefanar da makamashinta.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments