Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiRahotanni sun bayyana cewa har yanzu Boko Haram na cikin garin Ngoshe

Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu Boko Haram na cikin garin Ngoshe

Bayanai na nuna cewa mayaƙan Boko Haram na nan daram a garin Ngoshe.

Wasu rahotanni na nuna cewa har yanzu mayaƙan Boko Haram ke riƙe da garin Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno ta Arewacin Najeriya, kwanaki biyar bayan mummunan harin da suka kai garin wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji da fararen hula da dama.

Ma su tada kayar bayan sun sace sama da mata da ƙananan yara 100 a lokacin harin da suka kai ranar Larabar data gabata, bayaga sojoji da jagorori ciki harda babban limamin garin da suka kashe.

Wasu mazauna garin na Ngoshe da ke gudun hijira a Pulka, inda suka tabbatar da cewar har yanzu masu tada ƙayar bayan na cikin garin na su.

To sai dai wata majiyar tsaro ta ce ana nan ana ƙoƙarin ganin an fatattaki mayaƙan na Boko Haram daga garin.

Tun a ranar Larabar data gabata ne dai ƴan Boko Haram ɗin suka kwace garin na Ngoshe, kafin a ranar Juma’a su fito fili wajen yin iƙirarin kai harin.

Haka nan sun kuma bugi ƙirjin cewa sune suka yanke kan sojojin da suka kashe, tare da bayyana cewar a garin suke saran su gudanar da sallar Eidi.

Ɗaya daga cikin sojojin da ya tsallake rijiya da baya a harin, wanda kuma ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa a idonsa ƴan ta’addan suka yanka abokan aikinsa, sannan suka ƙona motocinsu da gidaje.

Najeriya dai ta kwashe tsawon shekaru tana yaƙi da ƴan ta’addan Boko Haram a shiyar Arewa maso Gabashin ƙasar, wanda ya haifar da asarar rayukan ɗinbin mutane.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments