Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTrump ya karɓi gawarwakin sojojin Amurka da aka kashe a rikicin Iran.

Trump ya karɓi gawarwakin sojojin Amurka da aka kashe a rikicin Iran.

Gawarwakin sojojin Amurka da Iran ta kashe sun iso Amurka, Trump ya jagoranci bikin girmamawa.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya halarci gurin da aka kawo gawarwakin sojojin Amurka na farko da suka mutu a yaƙin da Amurka ke yi da Iran.

An kawo gawarwakin sojojin dai a ranar Asabar zuwa sansanin sojin sama na Dover Air Force Base da ke jihar Delaware.

Dukkanin sojojin shida sun mutu ne a ranar Lahadin da ta gabata, bayan wani hari da jirgin yaƙi marar matuƙi na Iran ya kai tashar jiragen ruwa ta Shuaiba Port da ke ƙasar Kuwait.

Shugaban ya kuma gana da iyalan waɗanda suka mutu a sansanin Dover.

A lokacin wa’adinsa na farko, Trump ya taba halartar irin wannan taro sau da domin karrama sojojin Amurka da suka mutu a yaƙe yaƙen da ya gada daga shugabannin da suka gabace shi.

Sai dai a wannan karon, shugaban ya fuskanci sakamakon yaƙin da gwamnatinsa ta fara a Gabas ta Tsakiya, wanda har yanzu ba a ga ƙarshensa ba.

SourceDNN
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments