Rundunar Sojin Najeriya ta yi jana’izar sojojin da suka rasa rayukan su yayin fafatawa da ‘yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno
An gudanar da jana’izar ne a ranar Juma’a 6 ga watan Maris, 2026 a makabartar sojoji da ke Maimalari Military Cantonment a Maiduguri, babban birnin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba ya tabbatar da hakan.
Laftanar Kanar Sanni Uba ya sanar da jana’izar sojojin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 7a ga watan Maris 2026.
Da yake jawabi yayin jana’izar, kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya bayyana cewa akwai radadi a wannan rasuwa.
A cewarsa, aikin soja yana da lokutan farin ciki da nasara, amma akwai lokutan bakin ciki da ke tuna wa mutane irin farashin da ake biya wajen kare kasa.