Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai na musammanAn shafe kwanaki 10 ana zaman dar-dar a Zamfara bayan ’yan ta'adda...

An shafe kwanaki 10 ana zaman dar-dar a Zamfara bayan ’yan ta’adda suka dokar hana fita

Mazauna ƙauyen Bilbis da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara na rayuwa cikin matsananciyar fargaba, bayan da ’yan bindiga suka tilasta musu zama a gidajensu ta hanyar kakaba dokar hana fita.

Rahotanni sun nuna cewa ƙauyen, wanda shi ne asalin garin Sanatan da ke wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Ikira Aliyu Bilbis, ya koma wajen wahala da koke-koken neman taimako, sakamakon hare-haren ’yan bindiga da sace dukiya.

Wani mazaunin ƙauyen, Murtala Ahmed, ya bayyana cewa kusan sama da kwanaki goma ke nan al’ummar garin na cikin wannan halin takura sakamakon dokar hana fita da ’yan bindigan suka tilasta musu.

Ya ce duk wanda aka gani yana yawo a waje, ’yan bindigan kan tilasta masa komawa gida, sannan su yi amfani da damar wajen shiga gidaje suna bincike tare da kwashe kuɗi da sauran dukiyar mutane.

Lamarin ya ƙara tsananta ne a daidai lokacin da ake shirin shiga watan Azumin Ramadan.

Bayan da sojoji suka kai wani samame kan shanun ’yan bindiga a kusa da ƙauyen, an ce ’yan bindigan sun mayar da martani ta hanyar yanka shanun da suka jikkata, sannan suka tilasta wa kowane gida sayen wani ɓangare na naman a kan kuɗi Naira 5,000.

Bugu da ƙari, an kuma tilasta wa al’ummar garin biyan harajin kuɗi har Naira miliyan 30 domin a bar su cikin salama.

Mazauna garin sun ce tuni suka tara Naira miliyan 15 suka bayar domin rage barazanar hare-hare da zubar da jini.

A wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da aka wallafa a shafukan sada zumunta zuwa ga Sanata Bilbis, mutanen ƙauyen sun bayyana halin ƙuncin da suke ciki, suna cewa yawancin mazauna garin talakawa ne, kuma da dama ba su da kuɗin haya don guduwa zuwa wurare mafi aminci kamar Gusau.

A martanin rundunar ’yan sandan jihar, ta ce wata haɗaɗɗiyar rundunar haɗin gwiwa ta soja da ’yan sanda ta yi nasarar sake buɗe hanyoyin Kucheri zuwa Bilbis zuwa da Danjibga zuwa Keta.

Kwamishinan ‘yan sandan nihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya tabbatar da cewa rukunin ƙwararru kan kwance bama-bamai (EOD) sun gano tare da lalata bama-baman da aka binne a ƙasa (IEDs) da ‘yan ta’addan suka dasa don tare hanyar samar da abinci da zirga-zirga.

SourceIconic
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments