Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn kai hari da jirage marasa matuƙa kan matatar man Saudiyya.

An kai hari da jirage marasa matuƙa kan matatar man Saudiyya.

Matatar mai a Saudiyya ta gamu da hari ta sama, inda aka ga hayaƙi na tashi ba tare da ɓata lokaci ba.

Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da harin jirage marasa matuƙa kan matatan manta.

Saudiyya ta ce ta samu nasarar daƙile wutar da ta tashi a matatar bayan kakkaɓo jiragen marasa matuƙa.

Ma’aikatar makamashin ƙasar, ta ce an samu nasarar kashe wutar da ta matatar mai ta Ras Tanura – wanda kamfanin man ƙasar Aramco ke gudanarwa
Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran ƙasar ya wallafa, ya ce wutar ta yi wa matatar ”ƙaramar illa saboda ɓaraguzan” jiragen da aka kakkaɓo sun faɗa wasu wurare.

Yana mai cewa jami’an kashe gobara sun samu nasarar gaggauta kashe wutar.

Wani bidiyo ya nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe a saman matatar.

Saudiyya ta daɗe tana bai wa dakarun Amurka da na ƙasashen Yamma mafaka a ƙasarta, kuma a ranar Asabar gwamnatin ƙasar ta fitar da sanarwar Allah wadai kan hare-haren Iran.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments