Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNajeriya ta shawarci 'yan ƙasarta a Iran da ƙasashen Larabawa bayan harin...

Najeriya ta shawarci ‘yan ƙasarta a Iran da ƙasashen Larabawa bayan harin Amurka da Isra’ila

Najeriya ta gargadi ‘yan ƙasarta da ke zaune a Iran da ƙasashen Larabawa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya tana sa ido sosai kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, bayan matakan soja da Isra’ila da Amurka suka ɗauka kan Iran, da kuma hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai kan wasu wurare a wasu kasashen yankin Gulf.

An shawarci ’yan Najeriya da ke Iran da ƙasashen Gulf da ke makwabta su kasance cikin shiri da taka-tsantsan, su guji wuraren soji ko na gwamnati, kuma su rika kula da abin da ke faruwa a kewaye da su a kowane lokaci.

An kuma bukaci ’yan Najeriya su rage zirga-zirga da tafiye-tafiye marasa muhimmanci, su kuma guji tarurruka masu yawa, har sai yanayin tsaro ya daidaita.

An shawarci ’yan ƙasa su bi umarnin hukumomin ƙasashen da suke ciki, su kuma rika samun labarai daga sahihan kafofi, tare da guje wa jita-jita da labaran ƙarya.

Ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Tehran, Qatar, Bahrain, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Saudiyya suna cikin shirin ko-ta-kwana, domin ba da taimako, kuma Gwamnatin Najeriya ta jaddada cewa kare lafiyar ’yan kasarta a ƙasashen waje shi ne babban abin da ta fi ba muhimmanci.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments