Iran ta magantu kan hare-hare ta sama da kasashen Amurka da Isra’ila suka kai mata.
Kasar Iran dai ta lashi takobin mayar da martani ga hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai mata, inda ta yi alkawarin cewa Isra’ila zata gane kurenta.
Wani jami’in Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kasar na shirin kaddamar zafafan hare-haren ramuwar gayya.