Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHisba za ta fara hukunta matan da ke zama a gefen adaidaita...

Hisba za ta fara hukunta matan da ke zama a gefen adaidaita sahu

Hukumar Hisba na shirin hukunta mata masu zaman gefen adaidaita sahu

Hukumar Hisbah ta kammala shirye-shiryen fara aiwatar da dokar hana mata zama a gefen direban adaidaita sahu a Jihar Kano, da nufin ƙarfafa tarbiyya da kyawawan ɗabi’u a al’umma.

Daraktan wayar da kai na hukumar, Auwalu Ado Sheshe, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce za a gudanar da aikin tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin direbobi da masu adaidaita sahu domin tsaftace harkar sufuri da dakile abin da ya kira sabawa koyarwar addini.

Ya ce aikin zai maida hankali ne kan hana mata zama kusa da direbobin da ba muharramansu ba yayin hawa adaidaita sahu, tare da gargaɗin cewa duk wanda ya saɓa zai fuskanci hukunci.

Hukumar ta buƙaci direbobi da fasinjoji mata su bi umarnin, tana mai jaddada aniyarta na tabbatar da al’umma mai ɗabi’a ta gari bisa koyarwar Musulunci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments