Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHukumomin Rasha na yunƙurin haramta amfani da WhatsApp ga ‘yan ƙasa.

Hukumomin Rasha na yunƙurin haramta amfani da WhatsApp ga ‘yan ƙasa.

Rasha na shirin kakaba takunkumi kan manhajar WhatsApp a faɗin ƙasar.

Ƙasar Rasha ta yi yunƙurin toshe manhajar WhatsApp gaba ɗaya a ƙasar, in ji kamfanin manhajar yayin da gwamnatin kasar ke ci gaba da ƙara tsananta hana amfani da manhajojin tura saƙonni.

Kamfanin WhatsApp mallakar Meta ya ce wannan mataki na nufin tilasta wa masu amfani da manhajar fiye da miliyan 100 a Rasha su koma amfani da wata manhajar Gwamnatin kasar da za a iya saka wa ido.

Mai magana da yawun Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce Meta na iya ci gaba da aiki idan ta bi doka kuma ta shiga tattaunawa da gwamnati, amma ba za ta samu dama ba idan ta ƙi yin hakan.

Hukumar kula da intanet ta Rasha, Roskomnadzor, ta sanar da hakan ne a farkon wannan mako cewa za ta ƙara takaita damar shiga manhajar Telegram saboda rashin tsaro.

Telegram na da farin jini sosai a Rasha, musamman ma a tsakanin sojojin ƙasar a Ukraine.

Rasha ta jaddada cewa WhatsApp da Telegram duk sun ƙi adana bayanan masu amfani na Rasha a cikin ƙasar, kamar yadda doka ta tanada.

A cewar WhatsApp, kamfanin na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa mutane sun ci gaba da amfani da manhajar a kasar duk da ƙuntatawar da ake samu.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments