Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSama da mutum 100 ne suka tsere daga muhallansu a Kordafan na...

Sama da mutum 100 ne suka tsere daga muhallansu a Kordafan na Sudan – MDD

MDD ta bayyana cewa fiye da mutane 100 suka koma muhallin su a Sudan

Majalisar Ɗinkin duniya ta ce adadin ƴan gudun hijirar da suka tsere daga yankin Kordafan na Sudan mai fama da hare-haren mayaƙan RSF ya haura dubu 100 daga watan Oktoban bara kawo yanzu, a wani yanayi da yaƙi ke ci gaba da ta’azzara a yankin kudancin ƙasar.

Tun a cikin watan Afrilun 2023 Sudan ta faɗa yaƙin basasa mafi muni wanda ya ɓarke sakamakon taƙaddama kan madafun iko tsakanin Sojin gwamnatin ƙasar da dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF.

Yaƙin wanda aka bayyana da mafi muni da Sudan ta gani a tari ya sabbaba asarar dubban ɗaruruwan mutane tare da rana wasu aƙalla miliyan 11 da muhallansu.

Alƙaluman da hukumar ƙaurar baƙi ta Majalisar ɗinkin duniyar ta fitar a jiya Talata sun ce mutane aƙalla dubu 155 da 223 ne suka rasa matsugunansu a Kordafan waɗanda bisa tilasci suka fice daga gidajensu tsakanin ranar 25 ga watan Oktoban bara zuwa 5 ga watan Fabarairun da muke.

Baya ga miliyoyin ƴan gudun hijira da ke samun mafaka a yankunan da rikici ya lafa a cikin ƙasar ta Sudan, akwai kuma wasu da ke hijira a ƙasashen ƙetare ciki har da Sudan ta kudu da Somalia da Somaliland da Chadi akan gaba wadda ke ɗauke da mafi yawa na ƴan gudun hijirar.

Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana cewa rikicin na Sudan shi ne mafi tagayyara jama’a haka zalika mafi ta’zzarar buƙatar ɗaukin gaggawa.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments