Babbar kungiyar yaki da cin hanci da rashawa a duniya Transparency International (TI), ta sake sanya Najeriya a matsayi na 36 cikin kasashen da aka fi zargi da cin hanci a duniya a 2025.
Rahoton da aka fitar a shafin internet na kungiyar a ranar Talata ya nuna cewa Najeriya ta sauka daga matsayi na 140 a shekarar 2024 zuwa matsayi na 142 cikin kasashe 182 da aka tantance a 2025.
A tsarin jadawalin, matsayi na 1 na nufin kasa mafi tsabta daga cin hanci, yayin da matsayi na 182 ke nufin kasa mafi muni.
Duk da wannan koma-baya, Najeriya ta ci gaba da rike matsayi na 36 a jerin kasashen da aka fi zargi da cin hanci, da maki 26, kamar yadda ta samu a shekarar da ta gabata.
Najeriya ta yi kunnen doki da kasashen Kamaru, Guatemala, Guinea, Kyrgyzstan da Papua New Guinea, wadanda duk suka samu maki 26.
Rahoton ya kuma nuna cewa Denmark ta ci gaba da zama kasa mafi tsabta a duniya da maki 89, sai Finland da maki 88, Singapore da maki 84, da kuma New Zealand da maki 81.
Babu wata kasa daga nahiyar Afirka da ta shiga cikin kasashe goma mafi tsabta a duniya, domin jerin ya fi karkata ga kasashen Turai.
Ƙungiyar na tantance kasashen ne bisa hasashen yawan cin hanci da rashawa a bangaren gwamnati, ta hanyar amfani da rahotannin kwararru da kuma binciken ra’ayoyin yan kasuwa a fadin duniya.