Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShugaban hukumar aikin hajji ta ƙasa ya yi murabus

Shugaban hukumar aikin hajji ta ƙasa ya yi murabus

Shugaban hukumar aikin hajji ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya yi murabus.

Farfesa Abdullahi ya ajiye mukaminsa, a daidai lokacin da hukumar ke tsaka da shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa wani jami’i a cikin hukumar ya shaida cewa ajiye aikin na da nasaba da takardar korafi da Majalisar Kwamishinoni ta NAHCON ta aika wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Takardar ta kunshi zarge-zargen aikata ba daidai ba a kansa.

Jami’in ya ce:

“Takardar korafin da aka aika wa Shugaban kasa ce ta sa aka bukace shi ya ajiye aiki. Kowa ya san cewa hukumar na fama da takaddama da rikice-rikice tun bayan nadinsa.”

Ya kara da cewa ana sa ran Fadar Shugaban kasa za ta fitar da sanarwa nan gaba domin bayyana sunan sabon shugaban hukumar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments