Sunday, October 18, 2026
HomeLabarai'Yan bindiga sun kashe wasu sojojin Libya uku a wani hari

‘Yan bindiga sun kashe wasu sojojin Libya uku a wani hari

Yan ta’adda sun kashe sojojin Libya uku ya yin wani hari.

Dakarun gabashin Libya sun ce an kashe sojoji uku yayin da aka kama wasu a wani harin da aka kai wurin ƙetare kan iyaka na Al-Toum tsakanin Libya da Nijar.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ƴann bindigar sun kuma far wa Wadi Bougrara da Salvador kusa da kan iyaka da Nijar.

Sanarwar ta ce ‘yan bindiga masu aikata laifuka da suka hada fasa-ƙaurin kayayyaki’ ne suka kai harin, tana mai cewa dakaru sun bazama wuraren domin farautar maharan waɗanda bisa ga dukkan alamu sun tsere ta Nijar.

Tun da fari dai wata ƙungiyar ‘yan bindiga da ke kiran kanta “‘Yan juyin juya hali na Kudu” ta yi iƙirarin cewa ta karɓe iko da wurin ƙetare kan iyaka na Al-Toum tsakanin Libya da Nijar.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments