Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiZa mu yi duk mai yiwuwa don ceto mutanenmu da aka sace...

Za mu yi duk mai yiwuwa don ceto mutanenmu da aka sace – Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa zata yi duk mai yiwuwa don ceto mutan mutanan da aka sace

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Gwamnan ya ce yana bibiyar ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi game da batun, kuma ba zai gajiya ba har sai an yi nasarar ceto dukkan mutanen da aka sace.

A ranar Lahadi wasu mahara su ka shiga ƙauyen Kurmin Wali inda rahotanni ke cewa sun yi garkuwa da mutane fiye da 170 tare da jefa al’ummar yankin cikin ruɗani.

Da farko ƴan sanda da jami’an gwamnatin jihar Kaduna sun musanta faruwar lamarin amma daga baya suka fitar da sanarwar da ke tabbatar da shi, duk da cewa kawo yanzu babu haƙiƙanin bayani kan ko mutane nawa ne aka sace a ƙauyen.

Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta karkata ne ga aikin ceto mutanen, don haka sanin yawan su wani abu ne da zai iya zuwa daga baya domin a cewarsa masu ”siyasantar” da batun tsaro ne ke mayar da hankali kan yawan mutanen da aka sace.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments