Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroYan sandan a Borno sun yi nasarar kama mutane 65 dauke da...

Yan sandan a Borno sun yi nasarar kama mutane 65 dauke da makamai da kwayoyi

Rundunar yan sandan Jihar Borno sun yi nasarar kama mutane 65 da makamai da miyagun kwayoyi.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Borno ta kama mutane 65 da ake zargi da aikata laifuka tare da kwato makamai masu haɗari da miyagun ƙwayoyi a wasu sassan jihar.

Hakan dai na cikin sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a ranar Litinin 12 ga Janairu, 2026.

Sanarwar ta ce kamen ya biyo bayan wasu samame da ƴan sanda suka gudanar a ranakun 5 da 8 ga Janairu, 2026, bisa sahihan bayanan sirri, inda aka kai farmaki maboyar masu aikata laifuka.

Sanarwar ta ƙara da cewa daga cikin abubuwan da aka kwato akwai adduna biyar, wukake tara, tabar wiwi, wasu nau’o’in miyagun ƙwayoyi, shisha, da wasu abubuwa da ake amfani da su wajen aikata laifuka.

Rundunar ’yan sanda ta ce ana ci gaba da bincike kan waɗanda aka kama, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala binciken.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments