Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta tabbatar da zargin da aka yi na cewa ma’aikatan lafiya sun bar almakashi a cikin wata mata mai suna Aishatu Umar a lokacin tiyata, lamarin da ya yi sanadin rasuwarta daga bisani.
A cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar, babban Sakataren Hukumar Dr. Mansur Mudi Nagoda ya dakatar da ma’aikatan da lamarin ya faru a lokacin aikinsu tare da gabatar da batun a gaban kwamitin ladabtarwa.
Hukumar dai ta bayyana cewa ta dakatar da ma’aikata uku waɗanda suke da hannu a cikin lamarin nan take.
Sanarwar ta kara da cewa an miƙa batun zuwa kwamitin ladabtarwa ga ma’aikatan lafiya a jihar domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace waɗanda dokoki suka tanada.
Hukumar ta kuma miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiya Aishatu Umar kan abin bakin ciki da ya faru.
Hukumar ta tabbatar da cewa ba za ta lamunci kowane irin sakaci ba kuma za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin kare rayuka da kuma samun amincewar marasa lafiya a faɗin cibiyoyin lafiya na jihar.