Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKwankwaso ya taya Kiristoci murnar bikin Kirsimeti

Kwankwaso ya taya Kiristoci murnar bikin Kirsimeti

Tsohon gwamann Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP ya taya kiristoci murnar Kirsimeti

Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon Gwamnan Kano Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Kiristoci murnar bikin Kirsimeti.

Ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kwankwasoya kuma yi kira ga haɗin kai da jajircewa domin gina ƙasa mai ɗorewa.

Ya ƙara da cewa yayin da ake tunkarar shekarar 2026, akwai buƙatar shugabanni su kawo sabbin dabaru domin tallafa wa sojoji wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan, yana mai nuna kwarin gwiwa kan ƙarfinsu na cimma hakan.

Kwankwaso ya kuma yi fatan sabuwar shekara za ta kawo bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa da yalwar arziki ga al’ummar ƙasa baki ɗaya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments