Gwamnatin Amurka ta ce ta kai hare-haren sama kan wasu wuraren da ake zargin ‘yan ta’addar ISIS suna amfani da su a arewa maso Yammacin Najeriya, musamman a jihar Sakkwato.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya ba sojojin kasarsa umarnin kai harin, yana cewa harin yana da karfi kuma an kai shi ne kan ‘yan ta’adda.
Wannan shi ne karo na farko da sojojin Amurka suka kai hari a Najeriya tun bayan dawowar Trump kan mulki.
Rundunar sojin Amurka da ke kula da Afrika (AFRICOM) ta ce an kai harin ne bisa bukatar hukumomin Najeriya.
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya gode wa gwamnatin Najeriya bisa hadin kai da goyon bayan da ta bayar.
Ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya ta tabbatar da kai hare-hare kan wuraren ‘yan ta’adda, tana mai cewa manufar gwamnati ita ce kare rayukan dukkan ‘yan kasa, komai addininsu.
Ta kara da cewa ta’addanci a kan kowace al’umma abin Allah-wadai ne kuma barazana ce ga zaman lafiya a duniya.
A wani sakon da ya wallafa, Trump ya ce dalilin harin shi ne hare-haren da ‘yan ta’addar ke kaiwa kan fararen hula, musamman Kiristoci.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha musanta ikirarin cewa ana kai “kisan kare dangi” kan Kiristoci a kasar.