Wasu mazauna garin Jabo da ke Ƙaramar Hukumar Tambuwal a jihar Sokoto sun tsere daga gidajensu bayan wani abin fashewa ya tashi wuta a daren Alhamis.
Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba da tashin hankali, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
“Ina gida ne sai muka ji ƙara mai ƙarfi da ta girgiza wasu gidaje. Bayan abin ya faɗi a gefen garin Jabo, sai ya kama da wuta,” in ji shi.
Kasa da sa’o’i biyu bayan faruwar lamarin, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da kaddamar da wani babban farmaki kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Wani shaidan gani da ido, Attahiru Madawaki Jabo, ya shaida cewa abin fashewar ya tashi wuta ne bayan ya faɗi ƙasa.
Majiyoyi daga yankin sun ce sojojin da ke bakin wani shingen bincike kusa da wurin sun gaggauta zuwa wurin, suka killace yankin, sannan suka tattara sassan abin fashewar da suka warwatse suka kai su sansaninsu.
Wasu daga cikin mazauna garin sun ƙi komawa gidajensu saboda tsoron sake faruwar wani fashewa.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga jami’an tsaro ko gwamnati.