Kungiyar matasan jam’iyyar ADC ta bukaci dakatar da aiwatar da dokokin da ake shirin yi a farkon 2026 tare da neman mayar da su majalisa domin gyara.
Wata zanga-zanga da matasan ADC suka shirya ta nuna adawa da dokokin haraji na shekarar 2026, wadanda suka ce an sauya su bayan majalisar tarayya ta kammala aikinta.
Shugaban matasan jam’iyyar ADC, na kasa, Balarabe Rufa’i, ne ya jagoranci zanga-zangar, inda ya ce matasan kasar nan sun fusata da yadda aka kakaba dokokin ba tare da sahalewar jama’a ba.
Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa sababbin tanade-tanaden dokokin sun tauye hakkokin jama’a tare da bai wa jami’an haraji iko fiye da kima.