Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeBabban hafson sojin ƙasar Libya ya mutu a wani haɗarin jirgi

Babban hafson sojin ƙasar Libya ya mutu a wani haɗarin jirgi

Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan Majalisar ɗinkin duniya ta tabbatar da mutuwar babban hafson sojin ƙasar Janar Mohammed Ali Ahmed Al-Haddad a wani haɗarin jirgin sama da ya faru bayan tasowarsa daga birnin Ankara na Turkiyya a jiya Talata.

Jim kaɗan bayan tashin jirgin da ke ɗauke da babban hafsan da wasu manyan hadimansa 4 ne, Turkiyya ta bayyana cewa ta gaza bibiyar inda jirgin ya nufa, daga bisani aka samu tabbacin cewa jirgin ya faɗi ne sa’o’i kadan bayan tasowarsa.

Firaminista Abdul-Hamid Dbeiba ya bayyana mutuwar manyan jami’an a matsayin tashin hankali ga ƙasar, waɗanda ya ce suna kan hanyarsu ne ta dawowa daga tattaunawar da ke da nufin ƙawance da Turkiyya wajen ƙarfafa tsaro da samar da sababbin matakan tabbatar da tsaro a cikin ƙasar.

Firaministan Libya ya ce jirgin da ke ɗauke da Hafsan sojin ƙasar ya samu tangarɗar inji, kuma har kawo yanzu babu tabbacin adadin mutanen da ke cikin jirgin, sai dai bayanai sun ce Janar Muhammad al-Haddad ya yi balaguron tare da wasu muƙarrabansa 4.

Majiyoyin gwamnatin Libya sun ce babu ko mutum guda da ya tsira a cikin fasinjan, inda jirgin ya tarwatse sai dai yanzu haka ana ci gaba da bibiyar inda ya yi haɗarin don laluben gawarwakin da kuma tattaro ɓaraguzan jirgin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments