Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta Najeriya NCTC da ke ƙarƙashin ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ONSA ya bayyana masu hada-hadar tura kuɗi ta na’urar POS a matsayin waɗanda ke taimakawa wajen biyan ƴan ta’addan kuɗaɗen fansa da sauran ayyukan ƙungiyoyin ɓatagarin da ke sassan ƙasar.
Shugaban gudanarwar cibiyar Adamu Laka da ne sanar da hakan ga manema labarai a Abuja yayin jawabinsa na ƙarshen shekara, ya ce masu sana’ar ta POS na taimakawa ƴan ta’adda wajen gudanar da harkokinsu ba tare da barin sawun da za a iya bibiyarsu ba.
Kalaman na Adamu Laka wanda Manjo Janar ne a rundunar Sojin Najeriya, na zuwa a dai dai lokacin da ƙasar ke ganin ta’azzarar sace-sace mutane don neman fansa daga ƙungiyoyin ƴan ta’adda a sassa daban-daban ciki har da garkuwa da ɗalibai a makarantu da kuma masu ibada.
Ko a cikin watan Nuwamban da ya gabata, sai dai ƴan ta’addan suka yi garkuwa da ɗalibai a jihohin Kebbi da Neja kodayake an yi nasarar kuɓutar da ɗaliban daga bisani.
Duk da yadda gwamnatin Najeriya ta haramta biyan ƴan ta’adda kuɗi, amma iyalai da ƴan uwan waɗanda aka sace na biyan fansar don ƴantar da ƴan uwansu da ke hannun ɓatagarin, ta hanyar amfani da hanyoyin biyan kuɗin da baza a iya bibiya ba.
Haka zalika akwai zarge-zargen da ke nuna cewa ita kanta gwamnatin Najeriyar na biyan kuɗin fansa a ɓoye ga ɓatagarin don kuɓutar da mutanen da ke tsare a hannunsu.
A cewar Manjo Janar Laka, dukkanin binciken da suka gudanar ya nuna musu cewa ta hanyar amfani da POS ne ake tura kuɗin a kuma sassauya musu akawun daga wani waje zuwa wani da nufin kaucewa bin diddigi.
A cewar Mr Laka dukkanin bayanan da suka samu shi ne ƴan ta’adan kan bayar da lambar akawun ɗin banki ta masu POS wadda a nan ne ake tura musu kuɗi gabanin su umarci masu POS ɗin su sake tura musu wani akawun na daban tare da goge dukkanin hujjojin hada-hadar kuɗin da suka yi.