Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojojin saman Najeriya sun biya diyya ga wadanda harin kuskure ya shafa...

Sojojin saman Najeriya sun biya diyya ga wadanda harin kuskure ya shafa a Sokoto

Rundunar sojin saman Najeriya NAF ta biya diyya ga Iyalan da harin kuskure ya shafa

Sojojin saman Najeriya NAF sun ce sun biya diyya ga mutanen da iyalansu suka rasa rayuka ko suka samu rauni sakamakon harin sama na kuskure da aka kai a wasu kauyuka na Jihar Sokoto a ranar 25 ga Disamba, 2024.

NAF ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Lahadi.

Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa wani jirgin yaki na sojojin sama ya kai harin ne a lokacin da ake kai farmaki kan wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Lakurawa ne, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla fararen hula 10 a kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa, da ke Karamar Hukumar Silame a Jihar Sokoto.

An kai harin ne a karkashin hadin gwiwar aikin soja mai suna “Operation Fansan Yamma” da ke gudana a yankin Arewa maso Yamma.

A lokacin da lamarin ya faru, wani kakakin rundunar soji ya kare matakin, yana mai cewa mutanen da suka mutu na da alaka da kungiyar Lakurawa.

Kungiyar ta’addanci ta Lakurawa na yawan kai hare-hare ne a jihohin Kebbi da Sokoto.

Masana tsaro sun ci gaba da muhawara kan dangantakar kungiyar da sauran kungiyoyin ta’addanci.

Wasu na ganin Lakurawa na da alaka da kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaka da al-Qaeda, yayin da wasu ke cewa tana da nasaba da Islamic State a yankin Sahel.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments