Hukumomi a Najeriya sun ce an sako sauran dalibai 130 da aka yi garkuwa da su a jihar Neja.
Wasu ‘yan bindiga ne suka sace daliban da ma’aikatan makarantar ta Katolika ta Saint Mary a watan da ya gabata.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Sunday Dare a shafinsa na X ya sanar cewa: “A yanzu babu wani dalibi ko ma’aikacin makarantar da aka bari a hannun yan bindga.”
Mai makarantar kuma shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Neja, Bishop Bulus DauwaYohanna, ya bayyana cewa Gwamnan jihar Neja ya tabbatar masa da alamarin:
“Gwamna ya kira ni yanzu inda ya sanar da ni cewa an sako sauran ‘yan makaranta da malamai. Ya ce na zo na karbe su,” A cewar sa.